Labaran Duniya

Farashin Gari Da Jan Wake Yayi Tashin Gwauron Zabi A Najeriya

Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce farashin wake da tumatir da dankalin Turawa da gari da doya da dai wasu kayyakin abinci sun yi mummunan tashi a watan Yunin 2024.

NBS ta ce ta zaɓi wasu ne daga cikin kayan abincin sannan ta yi rahoto a kansu a watan Yunin 2024.

Rahoton ya gano cewa kilogiram ɗaya na jan wake ya ƙaru da kashi 252.13 cikin 100, wato ya tashi daga naira 651.12 a watan Yunin 2023 zuwa naira 2,292.76 a watan Yunin 2024.

“Jan wake ya rinƙa ƙaruwa da kashi 14.11 cikin ɗari a kowane wata a watan Yuni, ya zama naira 2,009.23 a watan Mayu 2024”.

Rahoton ya ce farashin dankalin Turawa ya karu da kashi 288.50 a shekara daga naira 623.75 a watan Yunin 2023 zuwa naira 2,423 a watan Yuni 2024.

Kilogiram na tumatiri ya ƙaru da kashi 320.67 cikin shekara ɗaya, daga naira 547.28 a watan Yunin 2023 zuwa 2,302.26 a watan Yunin 2024.

A cewar NBS kilogiram ɗaya na farin gari ya tashi da kashi 181.66 a shekara guda daga naira 403.15 a watan Yunin 2023 zuwa naira 1,135.51 a watan Yunin 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button