Labaran Duniya

Ba Mu San Inda Zanga-zangar Nan Za Ta Kai Mu Ba Cewar Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya nemi masu shirya zanga-zanga da su yi amfani da hanyoyin suka dace wajen neman mafita ga matsalolin da ƙasar ke ciki, maimakon shirin zanga-zanga.

Kashim Shettima ya bayar da wannan shawarar lokacin da ya sanar da shigar Najeriya cikin wani shiri na GCN, na samar da abinci mai lafiya da kawo ƙarshen fama da yunwa da matsalar abinci a duniya da ma Najeriya.

Mataimakin shugaban ya nemi a yi tunanin yadda za a kawo ƙarshen matsalolin da ƙasar ke fuskanta, ya kuma amsa cewa kasar na cikin mawuyacin hali saboda sauye-sauyen tattalin arzikin da suka gabatar, musamman sakamakon cire tallafin man fetur.

“Lokaci ne da ya kamata a yi tunanin shawo kan matsalar ta hanyoyyin da suka dace. Dimokradiyya ta bai wa ‘yan ƙasa damar su yi zanga-zanga a duka faɗin duniya, amma idan ka fara babu wanda ya san inda za ta ƙare, turba ce da za ta kai ƙasar ga yanayin rashin doka”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button