Amnesty Tayi Gargadi Akan A Daina Yi Wa Masu Shirin Fita Zanga-zanga Barazana
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta yi gargaɗin cewa yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ba tsari ba ne na dimokuraɗiyya.
Yekuwar zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, ta samu karbuwa a shafukan sada zumunta da kuma wasu ‘yan kasar.
Hukumomin Najeriya sun yi gargaɗi kan gudanar da zanga-zangar da za ta jefa ƙasar cikin tashin hankali tare da yin kwatanci da halin da ƙasashe kamar Kenya da Sudan da Libya ke ciki sakamakon yin bore.
Sai dai duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zanga ta lumana, amma shugaban kungiyar CISLAC kuma babban jami’i a kungiyar Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce “Dimukuradiyya ta ba ƴan ƙasa ƴancin fitowa su nuna damuwarsu.
TALLA
“Zanga-zanga tana ɗaya daga cikin tsarin mulkin ɗimokuraɗiyya da muke bi domin ko shi shugaban ƙasa na yanzu ta taɓa yin bara’a ga tsarin tafiyar da gwamnati.”
Yi wa masu zanga-zangar barazana, zai gurgunta nasarorin Shugaba Bola Tinubu da ya samu a baya,” in ji Rafsanjani.
Ya ƙara da cewa idan har gwamnati ba ta son a yi zanga-zanga, ya kamata ta gaggauta yin gyara.
“Ya dace a ce Gwamnati ta ƙara jaddada wa ƴan Najeriya cewa da gaske take yi wajen kawo gyara ga matsalolin da suka addabi ƴan Najeriya musamman tsadar rayuwa – wane tsari aka kawo da aka cire kuɗin tallafin mai,” in ji shi.
Ko Me gwamnati ke cewa?
Tun bayan da maudu’in da aka ƙirƙira mai taken “kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari a Najeriya’ a shafukan sada zumunta, gwamnati da manyan jami’an gwamnati ke bayar da shawara ga matasan da suka ƙirƙiri maudu’in su ƙara haƙuri, suna masu bayyana fargabar cewa wasu na iya amfani da zanga-zangar su cutar da al’umma.
Sun bukaci ƴan kasar da su kasance masu yin imani da gwamnatin APC mai mulki, tare da bayyana cewa shugaban kasa ya himmatu wajen magance matsaloli da damuwar ƴan Najeriya.
Gwamnatin ta kuma jaddada cewa babu wani ɓangare na hukuma da ke shirin hana ƴan ƙasa gudanar da zanga-zanga, kamar yadda mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya Ajuri Ngelale ya bayyana a hirar da aka yi da shi a wata kafar talabijin ta Najeriya ranar Lahadi.
“Babu wani a wannan gwamnatin da yake da ikon hana ƴan Najeriya ƴancinsu na yin zanga-zanga,” in ji Ngelale amma yana mai bayyana damuwa kan wasu da za su iya fakewa da zanga-zangar kamar yadda ta faru a zanga-zangar EndSars a 2020.
Ya ce gwamnatinsu na sane da harin da ƴan Najeriya ke ciki na matsin rayuwa, amma gwamnati na aiki domin magance matsalolin na yanzu da na nesa domin inganta rayuwa a ƙasar.