Labaran Duniya

Gwamnatin Najeriya Tace Zata Karya Farashin Shinkafa

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta karya farashin shinkafa wadda ta tanada da za a sayar a sassan kasar da nufin samar da sauƙi ga ƴan kasa.

A kasuwa dai ana sayar da buhun shinkafar ne kusan naira 80,000, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa wasu ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu da tsadar rayuwa.

Amma Gwamnatin tarayya ta ce za ta karya farashin shinkafar zuwa naira 40,000 kan duk buhu ɗaya mai nauyin kilogiram 50, kamar yadda ministan yada labarai na kasar Muhammad Idris ya shaida wa Manema Labarai.

Ya ce tuni aka ware wuraren da za a sayar da shinkafar a sassan jihohin Najeriya. Sai dai gwamnatin ba ta bayyana lokacin da za ta fara sayar da shinkafar mai sauƙin kuɗi ba.

Amma a cewar ministan, karya farashin na zuwa bayan gwamnatin tarayya ta bayar da tirelar shinkafa 20 ga duk jihohin ƙasar domin raba wa ƴan Najeriya.

“Da farko an bai wa gwamnoni shinkafa su raba wa masu ƙaramin ƙarfi kyauta kuma yanzu gwamnati ta tanadi shinkafa da za ta sayar da rahusa domin samar da sauƙi ga ƴan Najeriya,” in ji ministan.

Ya ce shinkafar da za a sayar a farashi mai rahusa ba wadda gwamnatin tarayya ta raba wa gwamnonin jihohi ba ce.

Shinkafa na ɗaya daga cikin abincin da ake ci a Najeriya, kuma farashinta a kasuwa kusan ya gagari aljihun wasu ƴan ƙasar.

Ministan ya ce gwamnati ta lura da tsadar shinkafar a kasuwa, shi ne ya sa ta ɗauki matakin samar da ita a farashi mai rahusa domin ƴan ƙasa su amfana

Kuma a cewarsa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.

“Idan aka ci gaba da kawo matakai irin waɗannan, sannu a hankali abubuwa za su yi sauƙi.”

A’ina za a sayi shinkafar?

Gwamnatin tarayya ta ce ta kafa kwamitoci a jihohin ƙasar da za su kula da tsarin sayar da shinkafar.

Ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce an tanadi cibiyoyi a jihohin ƙasar da za a sayar da shinkafar.

“An tanadi jami’an tsaro da za su sanya ido domin tabbatar da cewa ba a sayar da shinkafar fiye da farashin da gwamnati ta ƙayyade ba.”

“Kuma ana son waɗanda suka fi kowa buƙatar shinkafar ne za a sayar mawa idan har suna da halin da za su saya – kuma an dauki mataki na tabbatar da ba ta shiga hannun ɓata-gari ba,” in ji shi.

Sai dai duk da wannan albishir na gwamnatin tarayya, har yanzu wasu ƴan ƙasar na cewa gwamnonin jihohi ba su fara rabon shinkafar da gwamnatin ta yi ikirarin ta ba su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button