Kasar Faransa Ta Amince A Ba iWa Polisario Yanci
Faransa ta amince da shirin bai wa yankin yammacin Sahara ƴancin cin gashin kanta a ƙarƙashin ikon Morocco, a matsayin hanya ɗaya tilo ta warware rikicin da aka daɗe ana yi a kan yankin, kamar yadda shugaba Emmmanuel Macron ya bayyana a wata wasiƙa.
Wannan rikici da aka fara tun a shekarar 1997, ya sa an raba rana tsakanin Morocco, wadda ke ɗaukar wannan yankin na arewacin Sahara a matsayin nata, da ƙungiyar ƴan gwagwarmayar Polisario mai samun goyon bayan Algeria.
Faransa, wadda ita ce tsohuwar uwargijiya a wannan yanki, ta hoɓɓasa a diflomasiyance a tsakanin Morocco da Algeria a kan wannan batu, kuma tuni akasarin ƙawayen Faransa na yammacin Turai suka goyi bayan wannan shiri na Morocco.
Macron ya ce Faransa na kallon yankin yammacin Sahara a matsayin ƴankin Morocco na yanzu da kuma nan gaba, inda ya ƙara da cewa za ta yi aiki bisa turbar wannan matsayi a gida da waje.
Fadar sarkin Morocco ta yi maraba da wannan al’amari na goyon baya daga Faransa a kan iko da yammacin Sahara, a yayin da gwamnatin Algeria ta yi allah wadai da matsayin na Faransa, inda ta ƙara da cewa sakamako zai biyo baya, amma ba ta yi wani ƙarin bayani ba a kan haka ba.