Labaran Duniya
Masu Zanga-zanga A Jihar Zamfara Na Son A Inganta Tsaro
Daga Shamsu Bello Bungudu
Dandazon Mutane sun fito a sassa daban daban na jihar Zamfara domin yin Zanga Zangar Lumana wacce ake gudanar wa a Fadin Najeriya
Masu zanga-zangar dai sun fito a jihar Zamfara, daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da kangin matsalar tsaro.
Inda suka nemi gwamnati data samar masu da tsaro tare da kara yawan sojojin da ke aiki a jihar.
Kazalika, sun bayyana bukatarsu ta son komawa noma da hare-haren yan bindiga suka hana su yi gami da matsalar yunwa da suke fuskanta a Fadin jihar.