Kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta bukaci ‘yan sandan Nigeria da su karkata bindigogin su zuwa kan ‘yan ta’adda maimakon masu zanga zangar lumana.
Shugaban kungiyar na Kasa Joe Ajaero ya bayyana haka, yayin da yake kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya kawo karshen wadannan matsaloli da suka addabi jama’a da kuma biyan bukatun masu zanga zangar.
Mr Ajaero yace hanya guda ta warware wannan matsalar ta zanga zanga itace ta hanyar tattaunawa da shugabannin ta, maimakon barazanar da ‘yan sanda da kuma sojoji ke yi.
Mikiya Hausa Times Ta rawaito Shugaban yace sakamakon samun shaidun dake nuna cewar mutane sama da 40 suka mutu, ya zama wajibi su tuhumi yadda jami’an tsaron ke gudanar da ayyukan su.
Mr Ajaero yace da ‘yan sanda sun yi amfani da irin wannan karfin da ake bukata wajen kai hari a kan ‘yan bindiga da kuwa an shawo kan matsalar tsaron da ake fuskanta.
Akarshe Shugaban Kungiyar ta NLC ya bayyana damuwar kungiyar su dangane da asarar rayuka da kuma dukiyoyin da aka samu.