Labaran Duniya

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Yayi Allah Wadai Da Harbin Masu Zanga-zanga A Najeriya

Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai kan amfani da harsasai kan masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ya zargi jami’an tsaron ƙasar da harbin wasu masu zanga-zangar.

Atiku Abubkar ya ce harbin masu zanga-zangar lumana abin takaici ne, da ya yi kama da na lokacin mulkin kama karya na sojoji.

”Yana da kyau in tuna wa gwamnati da jami’an tsaro game da babban haƙƙinsu na tabbatar da tsaro ga ‘yan ƙasar da ke son gudanar da zanga-zangar, wadda ke cikin ‘yancinsu da kundin tsarin mulkin ya tanadar musu”, in ji Atiku Abubakar.

A lokacin zanga-zangar an samu rahotonnin harbi a jihohin Kano da Borno da Kaduna da wasu jihohin ƙasar.

To sai dai Atiku Abubakar ya ce, a duk lokacin da jami’an tsaro suka buɗe wuta kan masu zanga-zanga, to babu abin da hakan zai haifar illa tayar da yamutsi.

Tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyar PDP ya yi kira ga majalisar Dinkin Duniya da Kotun Duniya su sanya idanu kan abin da ke faruwa a Najeriya tare da tuhumar jagororin ƙasar da jami’an tsaro kan abin da suke aikatawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button