Labaran Duniya

Shugaba Tinubu Yace Gwamnatin Sa Ta Baiwa Jihohin Najeriya Fiye Da Naira Biliyan 570 Don Tallafawa Talakawa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa jihohin ƙasar 36 fiye da naira biliyan 570 don tallafa wa talakawansu.

Hakan na ƙunshin cikin jawabin da shugaban ƙasar ya yi da sanyin safiyar yau Lahadi.

Ko a kwanakin baya ma gwamnatin tarayyar ta ce ta bai wa kowace jiha tirela 20 ta shinkafa domin raba wa talakawan ƙasar, kodayake a baya-bayan nan wasu jihohin sun ce ba su samu kasonsu ba.

Haka kuma shugaba Tinubu ya ce masu ƙananan sana’o’i 600,000 ne suka samu tallafin bashi daga gwamnatin tarayyar.

Ya ƙara da cewa yanzu haka gwamnati na tantance masu matsakaitan sana’o’i mutum 75,000 domin samun bashin naira miliyan guda kowanennsu, da za su fara samu cikin wannan wata.

”Su kuwa masu manyan kamfanoni za mu ba su bashin naira biliyan ɗaya kowannesu don bunƙasa kasuwancinsu”, in ji shugaban ƙasar.

A ranar 1 ga watan Agusta ne dai wasu ‘yan ƙasar suka fantsama kan titunan ƙasar domin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da suke fuskanta a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button