Labaran Duniya

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ƴan ƙasarta masu shirin zuwa Birtaniya sanadiyyar zanga-zanga

Gwamnatin Birtaniya ta gudanar da taron gaggawa inda aka tattauna a kan yadda za a shawo kan hargitsi mai nasaba da kin jinin ƴan ci-rani a sassan ingila da kuma Arewacin Ireland.

Mako guda ke nan da mutane suka kai hari kan masallatai da otal-otal da kuma gidajen da masu neman mafaka ke zama.

Kazalika an balle shaguna da kuma jefa wa ƴansanda duwatsu.

Najeriya dai ta gargadi ƴan kasarta da ke shirin tafiya zuwa Ingila a kan su yi la’akari da abin da zai iya biyo baya.

Zanga -zangar da ake yi a kasar ta biyo bayan kisan da aka yi wa wasu yara mata uku a makon da ya wuce.

Mnistan cikin gidan Birtaniya, Yvetter Cooper, ya ce duk mutanen da suka yi tarzoma za su fuskanci fushin hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button