Labaran Duniya

Jami’an Sojin Najeriya Sun Nuna Nadama Akan Kisan Matashi A Zaria

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta nuna nadamarta kan yadda wani sojanta ya kashe wani daga cikin masu zanga-zanga a unguwar Samaru da ke Zaria a jihar Kaduna.

A wata sanarwa da darektan hulda da jama’a na rundunar sojin Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce rundunar ta samu kiran neman agaji ne cewa wasu bata-gari sun yi gangami a Samaru suna kona tayoyi a titi tare da jifan jami’an tsaro, daga nan ne aka tura sojoji domin su je su tarwatsa su tare da tabbatar da bin umarnin da gwamnatin jihar ta yi na dokar hana fita.

Nwachukwu ya ce zuwan sojojin ke da wuya sai gungun masu zanga-zangar ya fara kokarin kai wa sojojin hari, saboda haka ne ya ce wani soja ya yi harbi na gargadi, to amma harsashin sai ya samu wani yaro mai shekara 16 Isma’il Mohammed.

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka tsare sojan da ya yi harbin kuma ana gudanar da bincike a kansa.

Haka kuma kakakin ya ce shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriyar, Laftna Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ya tura wata tawaga ta musamman domin zuwa ta yi ta’aziyya ga iyalan matashin.

Sanarwar ta ce an yi jana’izar matashin tare da wasu manyan jami’an soji da suka halarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button