Labaran Duniya

Kasar Amurka, Masar Kuma Qatar Sun Nemi Hamas Da Isra’ila Su Koma Tattaunawar Zaman Lafiya

Ƙasashen Amurka, Masar da kuma Qatar sun fitar da sanarwar haɗin guiwa, inda suka yi kira ga Isra’ila da Hamas da su koma teburin tattaunawa domin tsagaita wuta tare da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza.

Sanarwar ta ce an tanadi abin da yarjejeniyar ta ƙunsa abin da kawai ya rage shi ne matakan da za a bi wajen aiwatarwa.

Isra’ila ta amince za ta halarci zaman a Doha ko a Alƙahira, sai dai Hamas ba ta ce komai kan hakan ba.

Batun cimma sabuwar yarjejeniyar diflomaisyyar na zuwa ne bayan da zaman ɗar-ɗar ya ƙaru a yankin na Gabas ta Tsakiya sakamakon kashe shugaban Hamas Isma’il Haniyeh a Tehran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button