An gudanar Da Sallar Nafila Da Addu’o’in Neman Saukin Rayuwa Da Matsalar Tsaro A Sabon Garin Kaura Namoda Dake Jihar Zamfara.
A yau Assabar ne al’ummar sabon garin Kaura Namoda kwansu da kwarkwata suka hadu a babban Masallacin juma’a na kusa NTA domin gudanarda Sallar Nafila da Addu’o’in neman saukin rayuwa da Kuma neman sauki akan matsalarda tsaro da ta zame masu karfen kafa.
Wani Shedun gani da Ido ya shedawa Manema Labarai Cewar “Mutanen sun hasune domin gudanarda wannan ibada domin isarda sakonsu zuwa ga mahaliccin kowa da komai domin ya share Masu hawayensu ganin yanda Abinci ke gagarar mutane da dama Kuma kullum ‘yan bindiga sai sun farmaki garin nasu”.
Haka zalika ya Kara da Cewar sunyi iya bakin kokarinsu na isarda sakonninsu ga hukumomi da lamarin ya rataya akansu Amma Babu wani abun azo agani Daya canza.
Shi dai wannan Zaman ya samu halartar mutane da dama musamman Matasan garin.