Labaran Duniya

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Mayarwa Da Obasanjo Martani Kan Batun Albashi

Majalisar dokokin Najeriya ta mayar wa tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo da martani game da kalamansa kan kudaden albashin ƴan majalisar

A ranar Juma’a ne tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo wanda ya sha sukar gwamnati ya yi zargi ƴan majalisar cewa su ke yankwa kansu albashi mai tsoka da kuma hanyoyin da suke samu kuɗi fiye da ƙima.

A cewar tsohon shugaban, hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya ce ya kamata ta yanke hukunci kan albashin da kowane ma’aikaci zai karɓa.

A martaninta, majalisar dokokin ta ce duk abun da ake ba wa ƴan majalisar na kan tsari tare da cewa ba su ke yankawa kansu albashi ba.

Amma a cikin wata sanarwa da Yemi Adaramodu, kakakin majalisar dattawa ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana ikirarin tsohon shugaban a matsayin “marar tushe”.

Sanata Lawal Adamu Usman ɗanmajalisa da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattawan kasar ya shaida wa BBC tare da rantsewa cewa “albashinsu bai kai miliyan daya ba.”

‘’Duk albashinmu gabaɗaya bai kai miliyan daya ba wallahi, idan kuma maganar alawus-alawus ne za a yi, sai dai mu ciyo bashi, saboda girman zirga-zirgar da nake yi daga Abuja zuwa mazaɓun da nake wakilta domin kowa na zuwa da buƙatarsa,” in ji sanatan.

Wannan cacar baki na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya.

A shekarun baya baya nan ɓangaren majalisar dokokin Najeriya na daga ɓangaren gwamnati da galibin mutane musaman ma masu sharhi kan al’amurran yau da kullum da ƙungiyoyin fararen hula ke zargin cewa abubuwan da suke samu na wuce ka’idar da ya kamata a ce ana ba su a matsayin haƙƙoƙinsu na yi wa alumma dokoki.

Wasu ƙungiyoyi da ƴan Najeriya sun ta nuna tsaya ga ƴan majalisar a kan zargin yadda suke laftawa kansu kudin mazaɓu a kasafin kuɗi wanda wasu ke ganin sun fifita kansu.

A wasu lokutan ma wasu ƴan majalisar da kansu sun fito sun koka kan cewa ana nuna bambanci a rabon kuɗin mazabun.

A yanzu kuma tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ne ya soki ‘yan majalisar kan cewar suna yankawa kansu albashi da kuma samun kuɗi masu gwaɓi daga fadar shugaban kasa.

‘’Kudin jarida, alawus din ɗan kamfai da kudin bahaya, kuma kuna ba kanku abubuwa barkatai, cikin girmamawa kun san hakan ba daidai ba ne a ce ina yankawa kaina albashi, majalisar dattawa na yin haka, har ma tinkaho kuke yi da haka’’ in ji Obasanjo.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa ana bai wa dukannin ‘yan majalisar naira miliyan 200.

Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sa ido kan harkokin Majalisun dokokin kasar ya ce akwai ƙamshin gaskiya a kalaman tsohon shugaban kasar:

‘’Akwai wasu kudade da a duk lokacin da za su tafi aikace-aikace ba ya cikin alawus -alawus dinsu, baya cikin albashinsu , hatta taron jin bahasin jama’a suna karbar alawus- alawus’’ in ji shi

Rafsanjaji ya yi gargadin idan har ba a kawo karshen wannan matsalar ba, to ba za a a daina rigimar siyasa da rigimar zabe ba. A cewarsa “idan mutane sun san cewa idan suka zo majalisa za su sami irin wadannan makuɗan kudade na Halak da na haram to za a ci gaba da samun rikici lokacin zabe”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button