Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki A Kasar Equatorial Guinea
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai bar ƙasar a ranar Laraba 14 ga watan Agusta domin ziyarar aiki ta kwana uku a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea, biyo bayan gayyatar da shugaban ƙasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya yi masa.
Ana sa ran ziyarar za ta karfafa alakar diflomasiyya da faɗaɗa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
A yayin ziyarar, Tinubu zai gana da shugaba Mbasogo domin tattaunawa da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da suka shafi man fetur da iskar gas da kuma ƙarfafa alaƙa ta tsaro.
Ana sa ran wadannan yarjejeniyoyin za su karfafa cin gajiyar tattalin arziƙin ƙasashen biyu.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa ne za su raka sa a ziyarar.
Ana sa ran tattaunawar za ta ba da damar yin hadin gwiwa a muhimman sassa, wanda zai amfani kasashen biyu cikin dogon lokaci.