Labaran Duniya

Majalisar Dattjan Najeriyai Ta Yi Wa Obasanjo Martani Akan Kalamansa

Majalisar dokokin Nijeriya ta mayar wa tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo martani game da kalamansa kan kudaden albashin ƴan majalisar.

A ranar Juma’a ne dai tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo wanda ya sha sukar gwamnati ya yi zargi ƴan majalisar cewa su ke yanka kansu albashi mai tsoka da kuma hanyoyin da suke samu kuɗi fiye da ƙima.

A cewar tsohon shugaban, hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya ce ya kamata ta yanke hukunci kan albashin da kowane ma’aikaci zai karɓa.

A martaninta, majalisar dokokin ta ce duk abun da ake ba wa ƴan majalisar na kan tsari tare da cewa ba su ke yankawa kansu albashi ba.

Sai dai ta cikin wata sanarwa da kakakin majalisar dattawa Yemi Adaramodu ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana ikirarin tsohon shugaban a matsayin “marar tushe”.

Wannan cacar baki na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya.

A shekarun baya baya nan ɓangaren majalisar dokokin Najeriya na daga ɓangaren gwamnati da galibin mutane musaman ma masu sharhi kan al’amurran yau da kullum da ƙungiyoyin fararen hula ke zargin cewa abubuwan da suke samu na wuce ka’idar da ya kamata a ce ana ba su a matsayin haƙƙoƙinsu na yi wa alumma dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button