Labaran Duniya

Al’uma Sun Fito Zanga-Zanga Bayan Ayyamq Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Venezuela

Hukumar zaben kasar da ‘yan adawa ke kallonta a matsayin wani bangare na jam’iyya mai mulki, ta ce shugaba Nicolas Maduro ne ya yi nasarar samun wa’adin mulki na uku, a zaben da aka gudanar a ranar 28 ga watan Yuli, da kasa da kashi 52% na kuri’un da aka kada.

‘Yan adawar siyasar kasar Venezuela da magoya bayansu sun tattaru a biranen kasar a ranar Assabar, don neman amincewa da abin da suka bayyana da gagarumar nasarar da dan takararsu ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar kusan makonni uku da suka gabata.

Hukumar zaben kasar da ‘yan adawa ke kallonta a matsayin wani bangare na jam’iyya mai mulki, ta ce shugaba Nicolas Maduro ne ya yi nasarar samun wa’adin mulki na uku, a zaben da aka gudanar a ranar 28 ga watan Yuli, da kasa da kashi 52% na kuri’un da aka kada.

Sai dai ‘yan adawa karkashin jagorancin tsohuwar ‘yar majalisar dokoki Maria Corina Machado, sun wallafa a kafofin yanar gizo, abin da suka ce kashi 83 cikin 100 na adadin kuri’un da aka kada, wanda ya baiwa dan takararsu, Edmundo Gonzalez goyon bayan kashi 67 cikin dari.

Zaben mai cike da cece-kuce ya jefa al’ummar kasar da ke fama da matsalar tattalin arziki cikin rikicin siyasa, kuma matakin da gwamnati ta dauka na murkushe masu zanga-zangar ya kai ga kame akalla mutane 2,400.

Rikicin da ke da nasaba da zanga-zangar kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 23.

Kasashen duniya sun ba da shawarwari masu yawa don shawo kan rikicin zaben, ciki har da gudanar da wani sabon zabe, amma yawanci jam’iyya mai mulki da ‘yan adawa duk sun yi watsi da su.

A babban birnin kasar, Caracas, dubban mutane ne suka taru a gabashin birnin tare da mamaye manyan titunansa.

A cikin sauran biranen kasar ma ‘yan Venezuela sun mamaye tituna. A Maracaibo, birni mai arzikin man fetur na Venezuela a arewa maso yamma, ɗaruruwan jama’a sun tarttaru tun da ƙarfe 9 na safe agogon ƙasar.

A garuruwan Valencia, San Cristobal da Barquisimeto, daruruwan mutane ne suka yi zanga-zanga, da yawa suna daga tutocin Venezuela, alamun zanga-zangar ko kwafin kuri’un da aka kada.

A Maracay da ke da nisan kilomita 110 yamma da birnin Caracas, kimanin masu zanga-zanga dari ne aka tarwatsa da hayaki mai sa hawaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button