Labaran Duniya
An Dukufa Wajen Aikin Ceto Na neman Mutum Shida Da Suka Nutse A Tekun Italiya
Masu aikin ceto a Italiya na neman wani ɗan kasuwar Birtaniya, Mike Lynch, da wasu mutane biyar da suka ɓace bayan wata guguwa mai karfi ta nutsar da jirgin ruwan da suke ciki a gaɓar tekun Sicily.
Matukin wani jirgin ruwan da ke kusa a lokacin da lamarin ya auku, Karsten Borner, ya taimaka wajen ceto wasu daga cikin waɗanda suka tsira.
Ya ce sun tarar da wani karamin kwale-kwale mai ɗauke da mutane 15.
“Mutum huɗu daga cikinsu sun jikkata, uku kuma sun ji munanan raunuka, mun ɗauke su zuwa cikin jirgin mu,” in ji shi.
Cikin ƴan kwanakin nan dai aka wanke Mike Lynch daga zargin zamba na biliyoyin daloli a Amurka sakamakon badakalar da ta dabaibaye sayar da kamfaninsa mai suna Autonomy.