Jam’iyar APC Ta Buƙaci Hukumar EFCC Ta Binciki Asusun ƙananan Hukumomin Jihar Kano
Jam’iyyar APC mai hamayya a jihar Kano, ta buƙaci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta rufe asusun bankunan ƙananan hukumomin jihar 44.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin jihar suka ce sun fara gudanar da bincike kan zargin kwangilar sayen magani a ƙananan hukumomin, inda ake zargin an bai wa ɗan uwan jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Cikin wata sanarwa da jam’iyar APC reshen jihar Kanon ta fitar mai ɗauke da sa-hannun shugabanta, Abdullahi Abbas, ta ce rufe asusun bankin ƙananan hukumomin ne kawai zai hana facaka da kuɗaɗen al’umma da sunan kwangila da kuma samun damar yin bincike.
Abdullahi Abbas ya ce ya kamata a gudanar da cikakken bincike kan badaƙalar da ake zargin an kashe maƙudan kuɗi wajen kwangilar samar da magunguna ga ƙananan hukumomin.
Sai dai a nata ɓangare jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar, ta ce abin da APC ke yi barin jaki ne tana dukan taiki.
Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Alhaji Hashim Dungurawa ya ce kamata ya yi jam’iyyar APC ta ce a binciki Ganduje kan zargin sayar da wasu filaye a jihar, da sauran laifukan da ake zargin gwamnatin APC da ta gabata a jihar ta aikata.
Ya ƙara da cewa ai abin da EFCC take yi shi ne abinda hukumar yaƙi da rashawa ta jihar ke yi, ”duk hukumomi ne da ke aiki bisa tsarin dokar”, kamar yadda ya shaida wa Manema Labarai.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karɓar korafe-korafe ta jihar Kano, ta ce ta gayyaci ɗan’uwan jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa Rabi’u Musa Kwankwaso, wato Musa Garba Kwankwaso wanda shi ne ake zargin an saka kuɗaɗen kwangilar sayen maganin a asusun bankin kamfaninsa.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimi Gado ya ce cikin waɗanda hukumarsa ta gayyatar har da babban sakatare a ma’aikatar ƙananan hukumomi da wasu daraktoci, kuma bayan bincikarsu sun ce su tafi za su zake nemansu nan gaba.