Labaran Duniya

Alƙalin Alƙalan Najeriya Ariwoola Yayi Ritaya A Yau Alhamis

Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya yi ritaya a ranar Alhamis, 22 ga watan Agustan 2024, bayan shafe tsawon lokaci yana aiki a ɓangaren shari’ar ƙasar, inda ya kai matakin ƙololuwa a aikin.

Ya riƙe muƙamai daban-daban a ɓangren shari’ar Najeriya.

Mista Ariwoola ya riƙe muƙamin alƙalin kotun ɗaukaka ƙara tsakanin 2005 zuwa 2011 bayan ɗaga darajarsa daga alƙalin babbar kotun jihar Oyo.

Sannan ya zama alƙalin Ƙotun Ƙolin ƙasar a shekarar 2011.

A cikin watan Yunin 2022 ne dai, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya naɗa mista Ariwoola Alƙalin Alƙalan Najeriya, a matsayin riƙon ƙwarya, bayan murabus ɗin tsohon Alƙalin Alƙalan ƙasar na wancan lokacin, Tanko Muhammad, bisa dalilai na rashin lafiya.

A watan Octoban 2022 ne kuma aka rantsar da shi a matsayin, bayan majalisar dattawan ƙasar ta tabbatar da shi.

Mista Ariwoola ya karanta fannin shari’a a jami’ar Ife da a yanzu ake kira (Jami’ar Obafemi Awolowo) Ile Ife, inda ya samu digirinsa na farko a fannin shari’a a shekarar 1980, sannan ya zama lauya a 1981.

A yau Alhamis, 22 ga watan Agusta ne ya cika shekara 70 a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button