Labaran Duniya

Kamfanin Oando Ya Kammala Sayen kamfanin Mai Na Agip Kan Kudi Dala Miliyan $783m

Babban Jami’in kamfanin Oando Plc, Wale Tinubu, ya ce mafarkinsu ya tabbata na mallakar kamfanin na Nigerian Agip Oil Company Limited (NAOC Ltd) wanda ya mallaki rijiyoyin mai da iskar gas yanzu ya zama na Oando.

Ansha zargi da yaɗa jita-jitar cewa kamfanin na Oando mallakar iyalan Tinubu ne lamarin da aka gaza kawo hujja, kodayake dai Wale Tinubu ne babban jami’in kamfanin,

Jaridar A Yau ta ruwaito yanzu Oando ya kara samun damar mallakar rijiyoyin mai na OMLs 60, 61, 62, da 63 daga kashi 20 zuwa kashi 40.

Mista Wale Tinubu ya nuna farincikinsu, domin sayen kamfanin zai jawo masu dumbin alkhairai, domin har ila yau, wannan ya kara yawan hannun jarin Oando a cikin dukkan kadarorin hadin gwiwa na NEPL/NAOC/OOL da suka hada da sabbin rijiyoyin mai da iskar gas guda 40 da aka gano, da kuma damar iko mallakar wasu bututun mai, da masana’antar sarrafa iskar gas guda uku,

Sannan da kuma tashar mai na Brass River, da tashoshin samar da wutar lantarki na KwaleOkpai 1 & 2 waɗanda ke da ikon samar da jimlar mega watt 960MW, da dai sauransu

Idan dai baku manta ba wani dan jarida mai bincike Bello wanda aka fi sani da  Dan Bello ya fallasa batun tun a kwanakin baya kafin yau da kamfanin ya sanar a hukumance

Sanarwar ta ce an gudanar da bikin kammala yarjejeniyar cinikin ne a otel din Peninsula Hotel dake London a yau Alhamis

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button