Labaran Duniya

Kasar Saudiyya Zata Shirya Taron Taimakawa Mutanen Najeriya Dakuma ƙasashen Sahel

Ƙasar Saudiyya ta ce za ta jagorancin shirya wani taro da nufin tara kuɗi don tallafa wa al’umomin ƙasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Burkina Faso da Mali da ke buƙatar tallafin jin ƙai.

Cikin wata sanarwar da cibiyar bayar da tallafi ta Sarki Salman ta fitar, ta ce za a gudanar da taron ne cikin watan Okbota da ke tafe.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum miliyan 33 ne ke buƙatar tallafi a yankin, ciki har da mutum miliyan 11 da aka raba da muhallansu a yankunan Sahel da Tafkin chadi.

Taron – wanda cibiyar bayar da agaji da Sarki Salman da ƙungiyar ƙasashe musulmai ta Duniya, OIC da ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira – za a shirya shi ne da nufin tara kuɗi da kayan agaji don magance matsalar jin kai da ake fuskanta tare da kare fararen hula a ƙasashen.

Ƙasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi sun shafe fiye da shekara 10 suna fama da rikice-rikice, lamarin da ya haifar da matsalolin zamantakewa da na tattalin arziki da asarar rayuka.

Sanarwar ta ce ‘yan gudun hijira da mutanen da suka rasa muhallansu ne kan gaba cikin waɗanda za su samu tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button