Labaran Duniya

Gwamnatin Jihar Neja Ta Nemi Agajin Sojoji Bayan ‘Yan Bindiga Sun Mamaye Wani Gari

Muƙaddashin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kai wa al’ummar garin Alawa – da ke yankin ƙaramar hukumar Shiroro – agajin sojoji.

A baya-bayan nan ‘yan bindiga sun mamaye garin tare da ƙwace iko da gidaje da gonakin mutanen yankin.

Rahotonni sun ce a watannin da suka gabata ne gwamnatin tarayya ta janye sojojin da ke aiki a yankin, matakin da ya ƙare kefa al’ummar yankin cikin ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga.

Kiran muƙaddashin gwamnan na zuwa ne kwanaki bayan da ranar Larabar da ta gabata ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari, tare da kashe manoma 13 da ke aiki a gonakinsu da ke wajen garin na Alawa.

Harin na baya-bayan nan ya sake jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali da firgaba, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin da dama barin yankin, don tsira da rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button