Labaran Duniya

Jami’an Yansanda A Benue Sun Kubutar Da Daliban Da Akayi Garkuwa Dasu

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce an kuɓutar da ɗaliban kiwon lafiya aƙalla 20 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue da ke tsakiyar ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar, Prince Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da hakan ranar Asabar.

“Muna tabbatar muku cewa an sako ‘yan’uwanmu ɗaliban kiwon lafiya 20 maza da mata da ma wasu ‘yan Nijeriya ranar Juma’a, 23 ga watan Agusta waɗanda aka yi garkuwa da su a dajin Ntunkon da ke jihar Benue,” in ji Mista Adejobi.

Rundunar ‘yan sandan ta ƙara da cewa ba ko kwabo ba a bayar a matsayin kuɗin fansa don sakin ɗaliban ba, saɓanin wasu rahotanni ke cewa an bayar da kuɗin fansa kafin sakinsu ba.

Mista Adejobi ya ce, “Haƙiƙanin gaskiya an ceto su su ta hanyar amfani da dabarun aiki da ƙwarewa. Muna godiya ga jami’an tsaro da mazauna yankin da lamarin ya faru, da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro bisa jajircewarsu”.

An yi garkuwa da ɗaliban ne, waɗanda ke cikin motocin bas guda biyu a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue a makon jiya a kan hanyarsu ta halartar wani taro a Enugu daga birnin Jos na jihar Filato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button