Hukumar Nema Tace Ambaliyar Ruwa Ta kashe Akalla Mutum 49 A Arewacin Najeriya Zuwa Yanzu
Aƙalla mutum 49 ne suka mutu a Najeriya sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar a jihohin arewa maso gabashin ƙasar, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa.
Kakakin National Emergency Management Authority (Nema), Manzo Ezekiel, ya faɗa cikin wata sanarwa a yau Litinin cewa jihohin Adamawa da Taraba na yankin ne da kuma Jigawa lamarin ya fi shafa, inda mutum sama da 41,344 suka rasa muhallansu.
A shekarar 2022, Najeriya ta fuskanci ambaliyar mafi muni cikin shekara 10, wadda ta yi ajalin mutum aƙalla 600, sannan ta raba miliyan 1.4 da muhallansu tare da lalata jimillar gonaki masu faɗin hekta 440,000.
“Yanzu ne muke shiga ƙololuwar damina, musamman a arewaci kuma lamarin ya tsananta,” a cewar sanarwar.
Zuwa yanzu ruwan ya lalata gonalki masu faɗin hekta 693 yayin da Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci.