Labaran Duniya

Kwamishinan Kudi Na Jihar Borno Alhaji Ahmad Ali Ahmad Ya Rasu

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da mutuwar Kwamishinan Kudi na jihar Alhaji Ahmad Ali Ahmad

A wata sanarwa da Kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida Farfesa Usman Tar ya fitar ta ce, marigayin ya rasu ne a cikin ɗakin sa.

Rahotanni sun ce an ɓalle ƙofar ɗakin sa ne bayan an ga ya wuce lokacin da ya saba fitowa, aka kuma yi ƙoƙarin tuntubarsa, amma ba a same shi ba.

Shi ne kwamishinan gwamnatin Borno na biyu da ya mutu a cikin shekara guda.

Domin ko a watan Oktoban 2023 ma kwamishinan gine-gine da sake tsugunar da mutane Injiniya Ibrahim Idriss ya rasu a jihar ta Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button