Shugabar ƙasar Tanzania Ta Radawa Zaki Sunan Madugun Adawar ƙasar
Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta rada wa wani fitinannen zaki sunan jagoran yan adawar kasar.
Lamarin ya faru ne lokacin da ta ziyarci wani gandun namun dawa na Tawa, kana aka gabatar mata da zakin da ya yi suna wajen kangara.
A yayin ziyarar ne dai, aka gabatar wa da shugaba Samia wannan zaki tare da ba ta labarin yadda ya zama gagarabadau, ya addabi jami’an gidan.
A lokacin ne kuma sai shugabar ta tambayi shin ko zakin na da suna?, aka ce a a, sai kuwa ta ce to a rika kiran sa da Tundu Lisu.
Mista Lissu dai, shi ne jagoran babbar jam‘iyyar adawar kasar da ake kira Chadema. Kuma an kama shi, tare da tsare shi a farkon wannan shekara, saboda yunƙurin gudanar da wani taro da ‘yan sanda suka ce na shirya da nufin tunzura jama’a.
To amma a cewar shugabar ta yi hakan ne domin da alama halinsu ya zo ɗaya. To shin ko ya Tundu Lisu ya ji da wannan al.’amari ?.
Da alama dai ya yi na’am da hakan ne, domin a wata hira da ya yi da kafafen watsa labaran cikin gida a Tanzaniyan, ya fito ne daga ahalin gwaraza, hasalima kakansa, ya taba halaka wani zaki da ya so kai masa hari da shanunsa a wajen kiwo.
Mista Lissu fitaccen mai sukar gwamnati ne kuma ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai masa a shekarar 2017.
Lokacin da aka buɗe wa motarsa wuta, harbi goma sha bakwai ya ratsa ta, amma duk da haka ya tsira. Ya tsaya takara a shekarar 2020, amma ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasar, marigayi John Magufuli.
Ms Samia, wadda ta kasance mataimakiyar shugaban ƙasa a lokacin, ta zama shugaba a shekarar 2021 bayan Mr Magufuli ya rasu yana kan mulki.
A shekara mai zuwa ne za a gudanar da zabe, inda shugaba Samia ke shirin sake tsayawa takara karo na biyu. Mista Lissu kuma ke shirin sake tsayawa takara don ƙalubalantar ta.