Kwamishinan Harkokin Makiyaya Da Sasanci Yayi Allah-waddai Da Rikicin Da Ya Faru A Neja
An yi kira ga al’umma da su daina ɗaukar doka a hannun su, wannan kiran ya fito ne daga bakin Kwamishinan harkokin makiyaya da sasanci na jihar Neja Alhaji Ahmad Sanda Rebe, inda ya ƙara da cewa duk wanda aka yi wa laifi ya kai ƙara wajen hukuma ko sarakuna da dai sauran masu ruwa da tsaki.
Tashar Sahel24 Tv ta ruwaito kwamishinan ya yi Allah-waddai bisa ɗaukar doka a hannu da wasu suka yi da ya kai ga kashe-kashen da aka yi a ƙauyukan Nabancita da Barkuta da kuma Beji.
Daga ƙarshe Rebe, yayi kira ga al’umma su daina ɗaukar doka a hannun su, su kai ƙorafi a inda ya dace idan an yi wa mutum ɓarna.
Wannan bayanai na kwamishinan dai na zuwa ne bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin makiyaya da Manoma a yankin Beji, inda hakan ya jawo rashin rayuwa ka a kowane ɓangare, inda kawo yanzu ba a kai ga tantance adadin da suka mutu a cikicin ba.