Labaran Duniya

Ƴan Najeriya 17 Sun Mutu Bayan Da Katanga Ta Fada Kansu A Wata Kasuwa Dake Kasar Nijar

Aƙalla mutane 17 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon rushewar wata katangar da ta fada a kansu a Kasuwar Yan Najeriya dake Maradi ta Jamhuriyar Nijar. 

Bayanai sun ce lamarin ya auku ne sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da tafkawa ba tare da ƙauƙautawa ba, wanda ba’a taɓa ganin irinsa ba. 

Hotunan bidiyon da RFI Hausa ta samu na nuna yadda mamakon ruwan da ake ci gaba da yi ke tafiya da kadarorin jama’a, ya yin da ake jin muryoyin jama’a na neman ɗauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button