Labaran Duniya

Babban Kwamatin Majalisar Dattawa Ya Nemi Arage W Yan Majalisar Najeriya Albashi

Babban Kwamatin Majalisar Dattawan Najeriya da ke nazari kan dokar zaɓe ya bayar da shawarar rage albashin ‘yanmajalisa da kuma masu muƙaman gwamnati.

Shugaban kwamatin, Sanata Sharafadeen Alli, shi ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin da yake ganawa da ‘yansiyasa da kuma wakilai a ɓangaren shari’a game da aikin kwamatinsa na yi wa dokar zaɓe ta 2022 kwaskwarima, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Najeriya suka ruwaito.

A cewarsa, suna ba da shawarar rage albashin ‘yanmajalisar da kashi 30 cikin 100, yayin da za a rage na masu riƙe da muƙamai da kashi 40 domin rage kashe kuɗin gudanar da gwamnati.

Yayin ganawar, jam’iyyun siyasa sun nemi a dinga gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa, da na ‘yanmajalisar tarayya, da gwamnoni, da ‘yanmajalisar jiha a rana ɗaya, suna masu cewa rarrabawar da ake yi yana jawo kashe kuɗi.

Jam’iyyun sun kuma nemi a haɗa katin zaɓe da lambar ɗan ƙasa ta NIN “domin ƙarin tsaro da kuma rage kashe kuɗi wajen yin rajistar katin zaɓe”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button