Labaran Duniya

Al’umar Musulmi Sun Fusata Biyo Bayan Soke Hutun Sallar Juma’a Ga ‘Yan Majalisa A Kasar Indiya

Gwamnatin wani lardi a Indiya ta soke hutun awa biyu da ake bayarwa ga ‘yan majalisa Musulmai a duk ranar Juma’a domin yin sallah, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a matakin tarayyar ƙasar a New Delhi.

Irin sauyin da aka samu a lardin Assam – wani lardi da ke arewa maso gabashin Bangladesh da China ya kawo ƙarshen wata al’ada wadda aka shafe shekara 87 wadda ake yi a Majalisar Dokokin Assam kuma ana zargin an yi hakan ne domin kawar da “ayyukan mulkin mallaka” waɗanda suka raba al’umma ta ɓangaren addini.

Sai dai wannan yunƙurin da alama ya ƙara zafafa rikicin ƙabilanci tsakanin ‘yan Addinin Hindu waɗanda su ne masu rinjaye da kuma Musulmai, wadda Indiya ce ƙasa mafi yawan Musulmai a duniya bayan Indonesia da Pakistan.

“Hutun na awa biyu lokaci ne wanda al’ada ne tsawon lokaci a Majalisar Assam. Duka abin da haɗakar jam’iyya mai mulki ta yi na cire wannan hutun ƙiyayya ce ga Musulunci,” in ji Ashraful Hussain, wanda ɗan majalisa ne daga jam’iyyar adawa ta All India United Democratic Front – wadda ita ce jam’iyya mafi girma da Musulmai suka fi goya wa baya.

A yayin da yake magana da TRT World, Hussain ya shaida ce babban ministan Assam wato Himanta Biswa Sarma na son cim ma manufarsa ta hanyar tayar da irin wannan ce-ce-ku-cen: ta hanyar goyon bayan masu tsatsauran ra’ayi ‘yan ƙabilar Hindu waɗanda a halin yanzu suka yi suka mamaye siyasa a matakin jiya da tarayya da kuma ajiye Musulmai a gurbinsu ta hanyar amfani da dabaru na rinjaye.

“Musulmi za su rinƙa yin sallolinsu, ko da hutu ko babu. Masu tsatsauran ra’ayi na son cin mutuncin Musulmi ne kawai,” in ji shi.

Kusan kashi 14.2 na Indiyawa biliyan 1.4 Musulmai ne. Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi gwamnatin Modi da bayar da shawarar “ƙiyayya da tashin hankali” a kan al’ummar musulmi fiye da miliyan 200, don haka canza halin da Indiya ke ciki.

Magoya bayan Jam’iyyar Bharatiya Janata Party (BJP), wadda take mulki a tarayya tun daga 2014, ana zarginsu da aikata laifukan ƙiyayya ga Muslmai waɗanda suka haɗa da rushe gidajensu da wuraren bautarsu.

Manazarta sun ce galibi ana nuna wariya ga musulmi a kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a duniya, wani lokaci a matsayin “Indiyawa marasa inganci” wadanda ake kallo ko dai a matsatin jikokin baƙi masu kutse ƙarnuka da dama da suka gabata ko kuma waɗanda suka kauce hanya da ya kamata su karɓi addinin Hindu na kakanninsu domin karɓar shaidarsu ta cikakkun ‘yan ƙasa.

A 2023, wani wurin bincike na India Hate Lab ya bayyana cewa an samu kalaman ƙiyayya 668 waɗanda aka yi su a kan Musulmai. Uku daga cikin huɗu na irin waɗannan lamuran an same su ne a jihohin da BJP ta mulka waɗanda suka haɗa da Assam.

Assam na daga cikin jihohin Indiya kaɗan waɗanda ke da adadi mai yawa na Musulmi. Ƙiyasin da aka yi ya nuna cewa kusan kaso 40 cikin 100 na mutanen Assam Musulmai ne — wanda wannan wani adadi ne da babban minista Sarma ya yi amfani da shi wurin ankarar da magoya bayansa kan cewa Assam na neman komawa jihar da “Musulmi ke da rinjaye”.

‘Yan majalisa 31 ne kacal cikin 126 ne Musulmai a Majalisar Dokokin Assam.

Babban Ministan Assam yana cikin shugabannin BJP guda uku waɗanda hukumar da ke sa ido kan kalaman ƙiyayya ta IHL ta ayyana a matsayin wanda ya gabatar da mafi yawan maganganun ƙiyayya a cikin 2023.

Sarma na amfani da tarihin Indiya a matsayin makami da kuma amfani da “dandamalinsa na mugunta” domin far wa Musulmai a kai a kai, in ji hukumar da ke sa idon.

Sai dai kuma, Sarma ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar jam’iyyar ‘yan ba ruwanmu da addini sai dai daga baya ya sauya ya koma jam’iyyar BJP ta Firaiminista Narendra Modi gabannin zaɓen 2016.

A yayin da yake magana da TRT World, mai magana da yawun Jam’iyyar All India Majlis-e-Ittehadul Muslimeen Waris Pathan ya bayyana cewa cire hutun Sallar Juma’a na daga cikin “yaƙin da ake yi kan Musulmi”, da Jam’iyyar BJP ta Hindu ke yi.

“Sun yi imani da siyasar ƙin jini. Sun tsani tufafinmu, sun tsani abincinmu, sun tsani karatunmu, sun tsani sallarmu, sun tsani kasancewarmu,” in ji Pathan, wanda jam’iyyarsa ke samun goyon baya daga waɗanda akasarinsu Musulmi ne da kuma ‘yan ƙabilar Hindu waɗanda talakawa ne a wasu jihohin India.

BJP na gudanar da siyasar “daɗaɗa wa ‘yan Hindu” ta hanyar kai Musulmi bango, kamar yadda ya ƙara da cewa.

“Abin da suka yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki. ‘Yancin yin addinin na cikin kundin tsarin mulki. Cin mutunci ne tsantsa masu rinjaye ke yi.”

A ɗayan ɓangaren, aƙalla jam’iyyu biyu na ƙawane na BJP — Janata Dal-United (JDU) da kuma Lok Janshakti — sun nuna rashin amincewarsu dangane da wannan mataki na soke hutun Sallar Juma’a, inda suka ce ya kamata babban ministan Assam ya mayar da hankali kan muhimman abububuwa da suka haɗa da kawar da talauci.

“Wannan matakin… ya saɓa wa ainahin manufofin kundin tsarin mulkin ƙasarmu,” in ji Neeraj Kumar, wanda jagora ne a JDU, wanda goyon bayansa na da muhimmanci ga ɗorewar gwamnatin Modi ta haɗaka.

Kakakin BJP Ajay Alok ya yi maraba da matakin da gwamnatin Assam ta dauka, yana mai cewa “an yi shi ne da yarjejeniyar kowa da kowa” a majalisar.

“Ga wadanda ke haifar da rudani kan wannan batu, ina so in yi tambaya mai sauki. A ina aka rubuta cewa a ba da hutun awa biyu na sallah a ranar Juma’a? Babu ko ina.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button