Labaran Duniya

Tsohon Ɗan takarar Dan Majalisar Jiha Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

Tsohon dan takarar majalisar jiha na karamar Hukumar Katsina kuma babban Jigo a jam’iyyar APC Hon. Abdurrazaq Ɗahiru, ya bayyana ficewar shi daga Jamiyyar APC tare da magoya bayansa sama da mutun dubu talatin 30,000 na kananan hukumomi 34 na fadin jihar Katsina.

“A cikin jawabin Hon. Abdurrazaq Ɗahiru, ya ce shi da magoya bayansa sun yanke shawarar fice wa daga jam’iyyar APC ne bisa dalilin gaza cika wa Talakawa alkawarin da jam’iyyar ta ɗaukar masu a lokacin yakin neman zaben 2023 duba irin wahalhalun da ‘yan kasa suke fuskanta na yunwa da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar kalubale wajen shan-suka daga ‘yan kasa sakamakon halin da jama’a suke ciki na tsadar rayuwa da matsalar tsaron da ta addabi al’umma a jahohin Arewa maso Yamma.

Abdurrazaq dai, jajirtaccen matashi ne da yake tare da jama’a wanda ya daɗe yana bada gudunmawarsa akan tafiyar Tinubu da Gwamna Radda kafin yabar APC.

Tabbas idan aka lura da irin gudunmawar da wannan matashin yake bayarwa a siyasa za’a iya cewa APC ta yi babban rashi a Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button