Labaran Duniya

Jami’an Hukumar DSS Sun Kama Shugaban NLC Na Najeriya

Hukumar Tsaro ta DSS ta kama Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), Kwamred Joe Ajaero.

Da sanyin safiyar yau litanin ne jami’an Hukumar DSS suka yi awon gaba da Kwamred Ajaero.

Majiyoyin tsaro a hedikwatar DSS da ke Abuja sun tabbatar wa Manema Labarai cewa Ajaero na hannunsu, domin amsa wadansu tambayoyi.

Wata majiya ta shaida mana cewa tsare Kwamred Ajaero na da nasaba da zargi da ake masa na dauƙar nauyin ta’addanci.

Ana iya tuna cewa a kwanakin baya, ’yan sanda sun tsare Kwamred Ajaero tare yi masa tambayoyi bayan sum zarge shi da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button