Labaran Duniya

Jami’ar Maiduguri ta dakatar da darussa da sauran harkokinta

Jami’a mallakin Jihar Borno ta dakatar da komai a Makarantar Nan take sakamakon ambaliyar da ta mamaye birnin na Maiduguri.

Sanarwar da Magatakardan jami’ar, Ahmed A. Lawan ya fitar ranar Talata ta kara da cewa an dakatar da karatu da sauran ayyuka har zuwa lokacin da za a fitar da sanarwa ta gaba.

Ya bayyana cewa yin hakan ya zama tilas domin kare rayukan dalibai da malamai da sauran ma’aikata da kuma nazarin halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button