Labaran Duniya

Matasan Garin Moriki Su byiyu Sun Kubuta Daga Hannun Turji

Daga: Barista Audu Bulama Bukarti

Allah madaukakin sarki Ya kubutar da matasan nan ‘yan Moriki da ke hannun Bello Turji wadanda yayi masu bidiyo jiya.

Turji yayi barazarar cewa zai kashe wadannan matasa gobe Jumu’ah in har mutanen Moriki ba su biya miliyan 30 din da ya daura musu ba. Bayan bidiyon, Turji ya canza sharawa ya ce zai kashe wadannan matasa da karfe 12:00 na ranar yau Alhamis idan ba a biya kudin ba.

Ko da jin haka wadannan matasa suka yanke shawara cewa su gudu cikin dare. Idan da sauran kwanakinsu su kubuta, idan kuma babu shikenan. Haka kuwa suka sulale cikin daren jiya suka gudu. Allah kuma ya kubutar da su. Dama Allah Yana taimakon duk wannan ya tashi, yayi yunkuri bakin iyawarsa. Yanzu haka uku daga cikin wannan matasa sun isa garin Moriki. Sauran biyun kuma, yanzu haka ana dakon isowarsu.

Amma har yanzu akwai mata guda shida ‘yan Moriki a hannun Turji. Amma su dama su bai ce zai kashe su ba tukuna. Muna fatan su ma Allah Ya kubutar da su. Allah Ya nuna mana karshen Turji da ire-irensa da masu gidansa da masu goya musu baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button