Shugaban TikTok, Shou Zi Chew, ya ce rufe dandalin zai saɓa wa dokar ‘yancin ra’ayi ta Amurka
A ranar 16 ga watan satumba, wata tawagar alƙalai na kotun ɗaukaka ƙara a gundumar District of Columbia Circuit za su saurari ƙorafin rukuni uku na mutanen da suka shigar da ƙara kan sabuwar dokar.
Su ne: ByteDance da reshensa na Amurka, TikTok Inc; rukunin jama’ar da ke amfani da dandalin; da kuma wata ƙungiyar siyasa mai tsattsauran ra’ayi mai suna BASED da ke samar da bidiyo a TikTok.
Masu ƙorafin sun ce tun da dai dubban Amurkawa na wallafa bidiyo a TikTok, rufe shi zai zama saɓa wa haƙƙinsu da tsarin mulki ya ba su na ‘yancin faɗin ra’ayi.
Shugaban dandalin na TikTok, Shou Zi Chew, ya faɗa wa masu amfani da dandalin: “Muna da ƙwarin gwiwa kuma za mu ci gaba da yaƙin kare ‘yancinku a kotu. Hujjoji da tanadin tsarin mulki na ɓangarenmu…Ku sani cewa ba za mu je ko’ina ba.”