Labaran Duniya

Kungiyar MSF ta ce mata da yara ba su samun kulawar likitoci a Darfur

Ƙungiyar agaji ta likitoci MSF ta yi gargaɗin matsalolin lafiya a yankin Darfur da ke Sudan.

Wani sabon rahoto da ƙungiyar ta fitar ya ce mata masu ciki 110 ne suka rasa rayukansu tsakanin watan Janairu zuwa Agustan bana, yayin da dubban yara ƙanana ke fuskantar yunwa.

Ƙungiyar ta ce sakamakon rushewar harkokin lafiya a yankin, mata masu ciki da jarirai na mutuwa daga cutukan da za a iya magancewa.

Kungiyar ta yi kira ga bangarorin su sasanta rikicin da ke tsakaninsu don kayan agaji da za su ceto rayuka su samu isa ga mutanen da suka rasa muhallansu.

Wakilin BBC ya ce MSF ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar an kawo ƙarshen wannan yaƙi, sannan bangarorin da suke yaƙi da juna su yi watsi da banbancin da ke tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button