Labaran Duniya

Zargin Ta’addanci: Kotu ta amince da tilastawa Gwamnatin tarayya binciken tsohon Gwamnan Zamfara

Jaridar Dimokuradiya ta ruwaito cewar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da karar da ke neman tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta binciki zargin alakanta Karamin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle da ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.

Ƙarar wanda dan rajin kare hakkin bil’adama, Abubakar Dahiru ya shigar, na da nufin gudanar da bincike kan zargin Matawalle da hannu a ayyukan ‘yan bindiga a lokacin da yake gwamna.

Takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1434/2024, ta bayyana shugaban kasa Bola Tinubu, da babban lauyan gwamnatin tarayya, da Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) a matsayin wadanda ake kara na 1, 2, da na 3, bi da bi.

Dahiru, wanda lauyansa Ojonimi Apeh ya wakilta, yana rokon kotun da ta bayyana cewa dole ne shugaba Tinubu ya umurci IGP ya binciki ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara, tare da mayar da hankali musamman kan zarge-zargen da ake yiwa Matawalle kan lamarin.

Mai shigar da karar ya ce a lokacin Matawalle yana gwamna (2019-2023), ‘yan fashi da makami sun karu zuwa matakin da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya sa dubban al’ummar jihar Zamfara suka rasa matsugunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button