Labaran Duniya

Kasashen Burkina Faso Da Nijar Sunyi Hani Kan Nuna Wani Shirin Fim Mai Suna The Bachelor

Kasashen Afirka ta Yamma na Burkina Faso da Nijar sun haramta kallon wani shiri na gidan talabijin na Faransa saboda “cin mutuncin” matan Afirka da kuma “saɓa wa dabi’u da al’adu” na ƙasashen biyu.

Wannan matakin dai ya yi daidai da matakin baya-bayan nan da kasashen biyu suka ɗauka – wadanda a baya Faransa ta yi wa mulkin mallaka – na haramta kallon kafafen yada labaran Faransa da dama.

A Wata sanarwa da babbar hukumar sadarwa ta gwamnatin mulkin sojan Nijar ta fitar ta ce an umarci gidan rediyon Faransa Canal da ya daina watsa shirye-shirye ko sake nuna shirye-shirye a zango uku na shirin The Bachelor.

Sanarwar ta ce shirin “na nuna ƙyama ga matan Afirka, da rashin kare matasa, kuma ya saɓa wa dabi’u da al’adun kasar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button