Aika-aika: Kotu ta ɗaure matashi bayan ya sace kayan abincin wani gida ya banka wa gidan wuta
An gurfanar da wani matashi a kotu kan sace kayan abinci a wani gida da kuma kone gidan a Jihar Kwara.
Hukumar tsaro ta Sibil Difens ta gurfanar da matashin ne kan satar kayan gidan, inda alkali ya tusa ƙayarsa zuwa Gidan Yarin Mandala da ke jihar.
Mai Shari’a na kotun Majistaren ya yanke hukuncin ɗaurin shekara guda ba tare da zaɓin biyan tara ba, bayan da ya samu matashin da laifi.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 26 ga watan Satumba 2024 ne matashin ya fasa gidan a cikin dare a yankin Onireke, Upper Gaa Akanbi, da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu.
Ya sace kayan abinci da kayan daƙi da sauransu, sannan ya banka wa gidan wuta.
Ya banka wa gidan wuta ne a kokarinsa na tserewa bayan jama’a sun yi yunkurin kama shi.
Amma daga bisani an yi nasarar kama shi aka damƙa wa jami’an Sibil Difens.
~~~Sahel24 Tv