Cutar Amai Da Gudawa Tayi Silar Rasa Rayuwar Mutun Bakwai A Jihar Kano
A jihar Kano, ana ci gaba da zaman makoki da alhinin rasuwar mutum bakwai waɗanda suka rasu a sakamakon cutar kwalara da suka kamu da ita bayan sun sha ruwan wata rijiya a wani ƙauye.
Bayanai na cewa lamarin ya auku ne sanadiyyar gurɓacewar ruwa sakamakon ambaliyar ruwa daga wani kudiddifi da ke kusa da rijiyar kuma kawo yanzu mutum fiye da 10 ne suke kwance a asibiti suna karɓar magani.
Bayanan daga ƙauyen Kanye da ke ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano na cewa mutanen garin sun fara ganin waɗanda suka harbu da cutar ta kwalara ne a unguwar da rijiyar take bayan da wasu magidanta suka yi amfani da ruwan rijiyar kuma suka kwanta rashin lafiya.
Kwamishinan lafiya na jihar ta Kano, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya ce ba shi da cikakken bayani tukuna, amma zai tura jami’ai don ƙara kai ɗauki da kuma bincike.
Sai dai bayanai na cewa a baya-bayan nan an samu mutuwar ɗimbin mutane a sassan jihar Kano sakamakon ɓullar cutar kwalara, inda hukumomi suka tabbatar da cewa cikin fiye da mutum 600 da ake fargabar sun kamu da cutar fiye da 30 ne suka mutu.
Ma’aikatar lafiya ta bayyana cewa ana kyautata zaton cewa ambaliyar ruwan da aka samu zuwa cikin wasu rijiyoyi ne ta haddasa kwalarar da ta yi sanadin mutuwar mutanen amma sun ce sun saka magani a wuraren.