Labaran Duniya

Ya Zama Tilas Mu Hukunta Wadanda Suka Chanye wa Ma’aikatan Mu Kudin  Goron Sallah

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ɗauki alwashin hukunta jami’an gwamnati da ke da hannu a almundahanar kuɗaɗen da aka ware domin bai wa ma’aikata goron sallah.

Wani rahotan jaridar Daily Trust ya ce gwamnan ya amince kan bai wa kowanne ma’aikaci da ke ƙarƙashin gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi ciki har da malaman makaranta kuɗi naira 30,000 a matsayin goron sallah.

Amma kuma ana zargin wasu daga cikin ma’aikatan musamman na ƙananan hukumomi sun karbi ƙasa da wannan adadin da aka tsara ba su.

“Wasu sun amshi naira 19,000 wasu kuma 20,000, yayin da wasu kuma har yanzu ba su samu nasu ba”, a cewar ɗaya daga cikin ma’aikatan da abin ya shafa yayin magana da Daily Trust.

Gwamnan a yayin da yake magana da ɗubbin magoya baya a gidan gwamnatin jihar a ƙarshen makon da ya gabata ya yi gargaɗi kan ma’aikatan da ke da hannun da su gaggauta dawo da kuɗin ko kuma su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button